Episode 1: Harshen Hausa - "The Hanyoyi Biyu".mp3

1:12
 
Chia sẻ
 

Manage episode 330525016 series 3353421
Thông tin tác giả Federal Republic of Nigeria Words of Life 8 được phát hiện bởi Player FM và cộng đồng của chúng tôi - bản quyền thuộc sở hữu của nhà sản xuất (publisher), không thuộc về Player FM, và audio được phát trực tiếp từ máy chủ của họ. Bạn chỉ cần nhấn nút Theo dõi (Subscribe) để nhận thông tin cập nhật từ Player FM, hoặc dán URL feed vào các ứng dụng podcast khác.
Hausa Language - "The Two Roads".mp3 // YAH 1Kalman Ya Zama Mutum1Tun fil'azal akwai Kalma, Kalman nan kuwa tare da Allah yake, Kalman nan kuwa Allah ne. 2Shi ne tun fil'azal yake tare da Allah. 3Dukan abubuwa sun kasance ta gare shi ne, ba kuma abin da ya kasance na abubuwan da suka kasance, sai ta game da shi. 4Shi ne tushen rai, wannan rai kuwa shi ne hasken mutane. 5Haske na haskakawa cikin duhu, duhun kuwa bai rinjaye shi ba.6 Mat 3.1; Mar 1.4; Luk 3.1,2 Akwai wani mutum da Allah ya aiko, mai suna Yahaya. 7Shi fa ya zo shaida ne, domin ya shaidi hasken, kowa yă ba da gaskiya ta hanyarsa. 8Ba shi ne hasken ba, ya zo ne domin ya shaidi hasken.9Akwai hakikanin haske mai shigowa duniya da yake haskaka kowane mutum. 10Dā yana duniya, duniyar ta wurinsa ta kasance, duk da haka duniya ba ta san shi ba. 11Ya zo ga abin mulkinsa ne, jama'a tasa kuwa ba ta karɓe shi ba. 12Amma duk iyakar waɗanda suka karɓe shi, wato, masu gaskatawa da sunansa, ya ba su ikon zama 'ya'yan Allah, 13wato, waɗanda aka haifa ba daga jini ba, ba daga nufin jiki ko nufin mutum ba, amma daga wurin Allah.14Kalman nan kuwa ya zama mutum, ya zauna a cikinmu, yana mai matuƙar alheri da gaskiya. Mun kuma dubi ɗaukakarsa, ɗaukaka ce ta makaɗaicin Ɗa daga wurin Ubansa.15Yahaya ya shaida shi, ya ɗaga murya ya ce, “Wannan shi ne wanda na ce, ‘Mai zuwa bayana ya zama shugabana, domin dā ma yana nan tun ba ni.’ ” 16Dukanmu kuwa daga falala tasa muka samu, alheri kan alheri. 17Domin Shari'a, ta hannun Musa aka ba da ita, alheri da gaskiya kuwa ta wurin Yesu Almasihu suka kasance. 18Ba mutumin da ya taɓa ganin Allah daɗai. Makaɗaicin Ɗa, wanda yake yadda Allah yake, wanda kuma yake a wurin Uba, shi ne ya bayyana shi.

93 tập